Alfijr
Alfijr ta rawaito an kama wata matashiyar yarinya ranar Lahadi 13/93/2022 da ke karyar gurgunta tare da zama kan keken guragu dubunta ya cika a jihar Lagos, mutane sun cika da mamaki bayan da aka tilsatawa yarinyar ta tashi tsaye daga kan keken guragun, kuma ya bayyana karara cewa ba gurguwa bace
An tilasta mata yin tafiya sannan mutanen da ke wajen suka dunga tunani kan yawan kudin da ta tara a wannan harkar
Yarinyar na zama ne a kan keken guragu wanda musamman ta tanade shi domin yin wannan harka da kuma yawo a yankin Ikeja tana rokon kudi daga hannun mutane a matsayin mai nakasa.
Alfijr
Lokacin da wasu matasa da suke lura da ita suka kama ta, sai suka tilasta mata sauka daga keken guragun sannan suka sa ta yin tafiya.
Tana sauka, sai ya bayyana karara cewa duka kafafuwanta guda biyu lafiya suke babu abun da ya same su.
Alfijr
Kamar yadda jaridar Lejit Hausa Ta rawaito