Yan Kwankwasiyya sun yi taron shan kayan marmari a Kano Don Murnar NNPP

Alfijr

Alfijr ta rawaito magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso sun gudanar da wani taro na shan kayan ƴaƴan lambu da nufin nuna goyon bayansu ga ƙoƙarin da Madugun ya ke yi na komawa jam’iyyar NNPP.

Tuntuni dai wasu daga cikin ƴan Kwankwasiyya su ka dangwarar da shahadar su ta jam’iyyar PDP, inda su ka koma jam’iyyar NNPP gabanin komawar madugun

Tuntuni dai wasu daga cikin ƴan Kwankwasiyya su ka dangwarar da shahadar su ta jam’iyyar PDP, inda su ka koma jam’iyyar NNPP gabanin komawar madugun.

Alfijr

A baya bayan nan dai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce har yanzu shi ɗan jam’iyyar PDP ne duk da cewa ya soma tattaunawa da jam’iyyar NNPP domin sauya sheka zuwa can.

A watan Fabrairu da ya wuce ne Sanata Kwankwaso ya jagoranci wani gagarumin taro na wasu manyan ‘yan siyasar kasar karkashin wata kungiya mai suna ‘The National Movement’, TNM.

Alfijr

Kamar yadda jaridar Kakaki Hausa Ta wallafa