Dubun Wata Mata Da Ta Sato Yara 9 Daga Dambatta Kano Za Ta Kai Su Ogun Ta Cika

Alfijr ta rawaito rundunar ’Yan Sandan jihar Kaduna ta kama wata mata dauke da yara tara a motar daukar kaya, daga karamar hukumar Danbatta da ke Kano, zuwa jihar Ogun da su.

Alfijr Labarai

Matar Dan ta debo yaran masu shekaru 10 zuwa 15, kuma matar ta nufi garin Ijebu-Ode da je jihar Ogun ne da su, kafin dubunta ta cika.

Kakakin rundunar yan Sanda jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige, ya ce sun tare motar ce a shingen bincike na Kurmin Mashi, bayan sun lura babu taga ko daya a jikinta, duk da cewa akwai mutane a ciki.

“Da misalin karfe 4:00 na yammacin Lahadi ne jami’anmu suka kama motar.

Alfijr Labarai

“Matar da yaran da ta sato yan a salon garin Dambatta, kuma ta ce ta dauko su ne don taya ta sana’ar siyar da abinci da take yi a jihar Ogun.

Kakakin ya ce za su ci gaba da bincike kan lamarin, kafin daukar mataki na gaba.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *