EFCC Ta Kame Wasu Ma aikatan Banki Su Goma Sha Biyu 12, Bisa Zargin Zamba

Alfijr ta rawaito hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC reshen jihar Enugu ta kama wasu ma’aikatan banki 12 a ranar Juma’a, 14 ga Oktoba, 2022 bisa zargin zamba cikin aminci.

Alfijr Labarai

Wadanda ake zargin sune: Odeniyi Anthony, Deki Kingsley Onyekachi, Oguchukwu Ene, Elendu Chizaram, Anyakora Uchenna, Onah Kingsley, Akwe Elizabeth da Chinenye Grace Acibe.

Sauran sun hada da: Victoria Ezedie, Chidi-Ukah Obinna, Etoh Lawrence Uzochukwu da Udeze Harrison.

Binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin sun sace wasu kudade a wasu asusu na kwana a reshen wani tsohon bankin da ke Enugu.

Alfijr Labarai

An karkatar da kudaden da aka sace daga asusun kwanan dalibai zuwa wasu masu cin gajiyar kudaden, inda tuni hukumar EFCC ta gano babban wanda ya ci gajiyar kudin.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *