Wani Mummunan Hadari A Motar Bus Ya Kashe Mutum 11 Ya Kuma Raunata Mutane 9


Alfijr ta rawaito Mutane 11 ne suka mutu, yayin da wasu tara suka samu raunuka daban-daban, yayin da wata motar tirela ta yi karo da wata motar bas mai mutane 18 a ranar Asabar a kauyen Hawan Jaki da ke Alkaleri kan hanyar Bauchi zuwa Gombe.

Alfijr Labarai

Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Bauchi Yusuf Abdullahi wanda ya tabbatar wa manema labarai afkuwar lamarin a ranar Lahadi a jihar, ya ce hatsarin ya rutsa da motocin kasuwanci guda biyu ciki har da wata motar Hiace mai lamba BA114-A28 mallakin kamfanin,Yankari Express na gwamnatin jihar Bauchi da tirelar DAF mallakin rukunin kamfanonin Dangote mai lamba JMU169XA.

Abdullahi ya bayyana cewa, tawagar ta FRSC ta garzaya wurin da lamarin ya faru jim kadan bayan samun rahoton inda aka kwashe su zuwa babban asibitin Alkaleri inda aka tabbatar da mutuwar tara daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.

Ya kara da cewa, “wasu wadanda suka jikkata sun mutu daga baya.”

Alfijr Labarai

Kwamandan ya yi kira ga masu ababen hawa da sauran masu amfani da hanyar da su kiyaye ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa tare da daina wuce gona da iri musamman a cikin wadannan Lokutan, saboda yawaitar zirga-zirgar ababen hawa a manyan hanyoyin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *