Farfesa Jega ya gargadi Najeriya dangane da cin bashin bankin IMF

Farfesa jega

Tsohon shugaban Hukumar Zaɓe ta kasa, farfesa Attahiru Jega ya gargaɗi gwamnatin Nijeriya da ta kauce wa karɓar shawarwari daga Bankin Duniya da Hukumar Bada Lamuni ta Duniya IMF.

Alfijir labarai ta rawaito Farfesa Jega ya ce kodayake yana da kyau a rika hulɗa da waɗannan hukumomin, amma dole ne gwamnatin Najeriya ta yi taka-tsan-tsan don gudun jefa ƙasar cikin gagarumar matsala.

Farfesan ya bayyana haka ne a yayin gabatar da maƙala a wani taron shekara-shekara na manyan darektoci da ke gudana a yanzu haka, yayin da a bana taron ke tattaunawa kan batun samar da ingantacciyar gwamnati domin farfaɗo da tattalin arziƙi.

Har ila yau, farfesa Jega ya buƙaci samar da sauyi a fannin zaɓen shugabanni, yana mai cewa, babban ƙalubalen da ke fuskantar Najeriya shi ne cewa, akasarin jagororin ƙasar ba su kintsa karɓar ragamar shugabanci ba.

Jawabin Jega na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ƴan Najeriya ke ci gaba da zargin Bankin Duniya da IMF da hannu wajen jefa ƙasar cikin mawuyacin matsin rayuwa a sanadiyar shawarwarin da suke bai wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Ƴan Najeriyar sun zargin IMF da tilasta wa shugaba Tinubu janye tallafin man fetur da kuma ƙarya darajar kuɗin ƙasar.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *