Gwamnatin Kano Ta Amince Da Biyan Karin Biyan  Mafi Karancin Albashi A Jihar

FB IMG 1715254046724

Gwamnatin Jihar Kano ta amince za ta biya N71,000 a matsayin albashi mafi karanci ga ma’aikatan jihar.

Alfijir labarai ta rawaito Gwamna Abba Kabir ne ya bayyana haka yayin karbar rahoton kwamitin tattaunawar ayyukan gwamnati karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan jihar a ofishinsa a ranar Talata.

Ya kara da cewa sabon albashin zai fara aiki daga watan Nuwamba 2024.

Sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta ambaci Gwamna Yusuf yana cewa, jihar Kano na daya daga cikin jihohin da ke da dumbin ma’aikatan gwamnati.

“Ina so in jaddada cewa Jihar Kano na da daya daga cikin jihohin masu mafi yawan ma’aikata a Najeriya, duba da irin yawan al’umarmu da bukatunmu na cikin gida da kuma matsi ta fannin kudaden shiga na gida da muka gada, mun yanke shawarar aiwatar sabon albashi na kasa akan N71,000.” Yusuf ya ce.

Gwamna Yusuf ya ce aiwatar da mafi karancin albashi zai kara wa jihar nauyin biyan albashi na wata-wata da sama da Naira biliyan 6, yana mai cewa za a nemi karin Naira biliyan 7 don bukatun kananan hukumomi 44 na jihar.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *