Gwamna Ganduje Ya Ki Amincewa Da Ajiye Aikin Wasu Daga Cikin Kwamishinoninsa

Alfijr

Alfijr ta rawaito gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya umarci Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Ali Haruna Makoda, da wasu Kwamishinoni uku da suka sanar da ajiye aikinsu, da su koma bakin aiki.

Wata sanarwar da Kakakin Gwamnan Kano, Malam Abba Anwar ya fitar ranar Talata, Ganduje ya amince da ajiye aikin Kwamishinoni guda shida.

Daga cikin Kwamishinonin da ya amince da ajiye aikin nasu akwai Nasiru Gawuna da Murtala Sule Garo da Ibrahim Abubakar Karaye da Mahmud Muhammad Santsi da Muntari Ishaq Yakasai da Musa Iliyasu Kwankwaso da kuma Kabiru Ado Lakwaya.

Alfijr

Gwamnan ya gode musu kan matukar gudunmawar da suka bayar wajen hidimta wa Jihar, tare da yi musu fatan alheri a nan gaba.

Ganduje ya umarci Manyan Sakatarorin ma’aikatun da lamarin ya shafa da su karbi ragamar tafiyar da su nan take.

Alfijr .

Kwamishinonin da Gwamnan ya umarta su koma bakin aiki sun hada Ilimi, Sanusi Sa’id Kiru da na Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Nura Muhammad Dankade da na Lafiya, Aminu Ibrahim Tsanyawa, da na hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar (KAROTA), Baffa Dan-Agundi wanda dama shi tuni Gwamna yaki amincewa da saukarsa.