Kasar Saudiya Ta Samar Da Mutummutumi Mai Bada Fatawa Da Turanci da Hausa A Harami

Alfijr

Alfijr ta rawaito babban Ofishin kula da harkokin masallatan Harami a Saudiyya ya samar da na’urar mutummutumi da zai riƙa bada fatawa da Turanci da Hausa a ɓangaren yin sallah ma mata.

An samar da na’urar a sauran sassan Masallacin Harami na Makka, inda za su riƙa bada bayanai a kan harkokin addini da ibada da kuma amsa tambayoyi da mata za su riƙa yinsu.

Sanarwar ta ce akwai yiwuwar za a ƙara wasu yarukan domin samun bayanai da fatawa cikin sauki.

Alfijr

Na’urar mutummutumin na ɗauke da allo mai tsayin inci 21 ɗauke da madannai na shafawa daban-daban, inda za a iya sarrafa na’urar da yaruka 11 da su ka haɗa da Turanci, Larabci, Faransanci, yaren Russia, Turkiya, Urdu, Malay, China, Bengali da Hausa.

An ɗora na’urar ne a kan turaku 4 masu tayoyi hade da wata fasaha ta tsayar da ita a kowanne lokaci.

Alfijr

Akwai kyamarori a gaba da bayan ta Sannan tana ɗauke da wajen saka na’urar jin magana a kunne, inda yanke ɗauke da lasifiƙa da kuma yanar gizo, wato Wi-Fi.

Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa