A wani mataki mai karfi don yakar ciwon Amosanin jini, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da wata sabuwar cibiyar lafiya mai inganci da za ta rika bayar da kulawa ta musamman kyauta ga masu fama da wannan cuta.
Alfijir Labarai ta rawaito Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da makon kula da lafiyar uwa da jariri na biyu a shekarar 2024 a karamar hukumar Kumbotso.
Sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta bayyana cewa cibiyar kulawar ta musamman tana cikin Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad.
Cibiyar za ta bayar da aiyyuka masu yawa kyauta, wadanda suka hada da gwaje-gwaje, shawarwari, bayar da magunguna, da kuma gudanar da ayyukan tiyata ga masu fama da ciwon sikila
Gwamna Yusuf ya dage wajen yaki da matsalar ciwon sikilane bisa alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabensa, kamar yadda aka bayyana a cikin tsarinsa na gyaran harkar lafiya.
A farkon shekarar nan, Gwamnan ya sanya hannu kan wani muhimmin kudirin doka na gwajin lafiya kafin aure, wanda ya haramta auratayya tsakanin masoya da suke da irin wannan nau’in kwayoyin halitta (genotype) a jihar, domin hana haihuwar ‘ya’ya da ciwon sikila.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj