Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya naɗa sababbin sarakuna masu daraja ta biyu a jihar.
Alfijir labarai ta ruwaito waɗanda aka naɗa ɗin su ne Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin Sarkin Gaya, wanda kafin naɗinsa shi ne tsohon Sarkin Masarautar Gaya da aka rushe.
Sai Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin Sarkin Karaye, wanda kafin naɗinsa shi ne hakimin Rogo.
Sai kuma Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin Sarkin Rano, wanda kafin naɗinsa shi ne hakimin Bunkure.
Wata sanarwa da kakakin gwamnan na Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce naɗin ya fara aiki nan take.
“Yayin da yake musu murna bisa naɗin, Gwmana Abba ya yi kira a gare su su kasance masu kiyaye al’adu da zaman lafiya da haɗin kan jama’arsu.
Sababbin masarautun za su ƙunshi wasu ƙananan hukumomi ne a ƙarƙashinsu, sai dai yawan ƙasashen hakiman bai kai na tsofaffin masarautun da aka rushe ba.
Sanarwar ta ce a yanzu “Masarautar Gaya za ta ƙunshi ƙananan hukumomin Gaya da Ajingi da Albasu ne kawai.
Rano za ta ƙunshi ƙananan hukumomin Rano da Kibiya da Bunkure kawai.
Ƙaraye za ta ƙunshi ƙananan hukumomin Ƙaraye da Rogo kawai.”
Naɗa sabbin sarakunan na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da tirka-tirka kan dokar da gwamnatin jihar ta sanya wa hannu ta rushe masarautu hudu na Gaya da Rano da Karaye da kuma Bichi, da sauke Sarki Aminu Ado Bayero da kuma mayar da Sarki Muhammadu Sanusi na II.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj