Gwamnan Kano ya gwangwaje wasu kungiyoyi 28, da buhunnan shinkafa 100 Taliya 100 da kuɗin cefane 20k ga kowane mutum

IMG 20260316 WA0172

Mai girma gwamna jahar kano Alh Abba Kabir Yusuf ya tsunduma al-ummar jahar kano cikin alkhairin “KANO FIRST END OF RAMADAN SUPPORT” dumu dumu, da buhun shinkafa dana taliya da kuma tsabar kuɗi naira dubu ashirin ₦20,000

Wanda dan amanar gwamnan Kwamishinan kasa da tsara buranen jahar kano ya tabbatar da wakilcin  kaddamar da rabon kamar yadda Gwamnan ya wahale da a yiwa ƙungiyoyin al’umma na kasa da wasu hukumomin addini da ba safai ake ake tunawa da su a irin wannan tallafin ba.

Ƙungiyoyin da ma’aikatun sun haɗa da :

1 Nigeria Correctional Centre Imams
2 Hukumar Zakkah
3 Hukumar Sharia
4 Hukumar Hisbah
5 Imams Other Security Agencies
6 Kano State Council of Imams
7 Daawah Group of Nigeria
8 Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah
9 Kungiyar Sha’irai
10 Nigeria Aid Jama’atul Nasaraul Islam
11 Council of Quranic & Islamiyya Schools
12 First Aid Group of Fityanul Islam of Nigeria
13 Fadar Sarkin Guragu
14 Nigerian Association of Blind – Kano Chapter
15 Kano State Association of Deaf
16 Kano State Grave Attenders Association
17 Voice of Widows, Divorcees & Orphans Association
18 Women and Orphan Development Association
19 Gamayyar Kungiyoyin Da’awah ta Musulunci
20 Kungiyar Mahaddata Al-Qur’ani
21 Tijjaniyya (Sheikh Ali Bichi)
22 Sheikh Auwal Tijjani (Commissioner)
23 Izala (Malam Usamatu Salga)
24 Gwani Auwal Mukhtar
25 Tsangaya (Gwani Musa Falaki)
26 Kadiriyya (Sheikh Bazallahi Sheikh Nasir Kabara)
27 Kungiyoyin Fulani 44 LG
28 Kungiyoyin Yan Fansho

Wadannan sune kadan daga cikin wanda zasu rabauta da wannan tallafin, kuma ko wacce kungiya ko hukuma an ware mata shinkafa buhu 100, Taliya 100, da dubu 20, 000 na Mutum darin

Allah ya sakawa gwamna Abba Kabir Yusuf da alheri shima farin jakadan amanar balaraben gwamna Abduljabbar muna masa fatan alheri Allah ya mai da koko masauki.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *