Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da jita-jitar da ke yawo a wasu kafafen yaɗa labarai da kuma shafukan sada zumunta da ke iƙirarin cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, zai jagoranci hawan sallah mai zuwa.
Gwamnatin ta bayyana cewa rahoton ba shi da tushe kuma ba’a yanke wani hukunci a hukumance game da lamarin ba. Ta ƙara da jaddada cewa batun masarautar Kano yana gaban kotu a yanzu, don haka yana da muhimmanci a bari ɓangaren shari’a ya gudanar da ayyukansa ba tare da matsin lamba ko kawo ruɗani a cikin al’umma ba.
A halin yanzu, gwamnatin jihar Kano ta kasance a tsaka-tsaki kuma ta nisanta kanta daga dukkan ɓangarorin biyu dake taƙaddamar masarautar har sai kotu ta yanke hukunci na ƙarshe wanda doka ta amince da shi.
Gwamnatin Jihar Kano ta kuma yi kira ga jama’a da su cigaba da bin doka, su guji yaɗa jita-jita, sannan su tabbatar da cewa sun sami sahihan bayanai ne kawai daga majiyoyi masu tushe masu inganci da na hukuma.
Bugu da ƙari, gwamnati ta buƙaci kafofin yaɗa labarai da masu amfani da kafofin sada zumunta da su tabbatar da sahihancin duk wani labari kafin su yaɗa shi, domin guje wa haifar da ruɗani ko tashin hankali a cikin al’umma, musamman yayin da bukukuwan Sallah ke gabatowa.
Gwamnatin ta sake jaddada alƙawarinta na wanzar da zaman lafiya, haɗin-kai, da kwanciyar hankali a faɗin jihar Kano.
Sa Hannu.
Kwamishinan yaɗa labaran jihar Kano, Hon. Ibrahim Abdullahi Waiya,
Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar Kano.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t