Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da kwamitin bincike kan zargin kashe-kashe da lalata dukiyar al’umma a yayin zanga-zangar #EndBandGovernance da aka gudanar a watan Agusta da ya gabata.
Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnan ya kaddamar da kwamitin na mutane 14 yau Litinin a gidan gwamnatin jihar.
Mambobin kwamitin sun hada da:
1. Justice Lawan Wada Mahmoud (Rtd)…shugaban kwamitin
2. Barr. Tajuddeen Funsho…Mamba
3. Alh. Sani Isa…Mamba
4. Dr. Musa Borodo…Mamba
5. Barr. Sagir S. Gezawa…Mamba
6. ACP Munnir Madugu…Mamba
7. Shehu Abdullahi…Mamba
8. Hajiya Gambo Abdullahi…Mamba
9. Amb. Ibrahim Waiya…Mamba
10. Dr. Said Ahmad Dukawa…Mamba
11. Revd Murtala Mati Dangora…Mamba
12. Barr. M. B Dan-azumi…Mamba
13. Barr. Haruna M. Muhammad…Mamba
14. Salisu Marmara…daga ma’aikatar shari’a a matsayin Sakatare.
Gwamnan ya hore su da su tabbatar da yin aiki na hakika ba tare da almundahana ba kuma su kawo rahoto a lokacin da aka diba musu.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj