Gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, ya nesanta kansa daga zargin cewa gwamnatinsa ta raba wa mata Dan kamfai ja a matsayin tallafi, yana mai cewa abin da ya faru, ya faru ne ba tare da saninsa ko amincewarsa ba..
Gwamnan ya musanta cewa da saninsa kan lamarin, sannan ya gabatar da waɗanda suka jagorajci daga Dan kamfen, Teema Cool, da mukarrabanta a gabansa yayin addu’a da aka gabatar a gidan gwamnati domin yi musu nasiha kan abin da suka aikata.
Yusuf ya kara da cewa, “Mun ji abin da ya faru. Muna cikin harkokinmu sai aka sanar da ni cewa wasu mata sun fito da wasu abubuwa… Gwamna bai sani ba. Na ma daina amfani da kafafen sada zumunta saboda irin wannan abu. Na fi son a rika kawo min irin wannan bayani kai tsaye.”
Ya kara da cewa dole ne a yi Allah wadai da lamarin domin ya sabawa al’ada da koyarwar Musulunci.
Gwamnan ya ce da ya samu labarin abin da ya faru, ya gayyaci matan domin su bayyana kansu.
Daga bisani, an ga matan suna karanta Alƙur’ani mai girma tare da yin addu’o’i da neman gafara kan abin da suka aikata.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t