Gwamnan Kano yayi kyakkyawan gargadi ga malamai akan dalibansu

FB IMG 1723959647845

Gwamnan jihar Kano Eng. Abba Kabir Yusuf  ya gargadi malamai da su daina tilastawa dalibai yin aikace-aikacen wahala a ciki ko a wajen makaranta

Haramcin na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a ranar Lahadi. 

Gwamnan ya jaddada cewa makarantu wuraren karatu ne da tarbiyya, ba wuraren yin aikin wahala ba. 

Yayin wata ziyarar bazata da ya ka makarantar koyon harshen larabci (School for Arabic Studies) Kan, gwamnan ya tarar da wasu dalibai suna tonon ramin bututun bayan gida. 

Inda cikin fushi, gwamnan ya tambayi shugaban makarantar dalilin da ya sa aka ba dalibai irin wannan aiki. 

Shugaban makarantar ya shaidawa gwamna cewa aikin an ba su ne bayan an tashi daga makaranta.

Sai dai nan take gwamnan ya bayar da umarnin dakatar da yaran daga aikin, ya kuma  tabbatar wa shugabannin makarantar cewa gwamnatinsa za ta gyara dukkan gine-ginen da suka lalace, har da masallacin da ke cikin makarantar. 

Haka kuma, ya bada umarni cewa duk wata bukata ta gyaran makaranta a mikata ga Ma’aikatar Ilimi ko ofishinsa domin aiwatarwa.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp 👇👇

https://chat.whatsapp.com/FNMJaJ3I8Sc0bkkm8aJQbQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *