Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa ta kammala dukkan shirye-shirye da suka dace don gabatar da kasafin kuɗi na farko a tarihin jihar mai darajar Naira triliyan 1 na shekarar 2026.
A yayin bude Taron Majalisar Zartaswa Gwamna Yusuf ya ce girman wannan kasafi yana nuna azancin gwamnati wajen aiwatar da manyan ayyuka, gyaran birane, da fadada ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Ya bayyana cewa karuwar kasafin kuɗin na shekarar 2026 ta samo asali ne daga inganta hanyoyin samun kudaden shiga na cikin gida da kuma dakile duk wata asarar kudade, wanda hakan zai ba gwamnati damar aiwatar da manyan ayyuka masu sauyi a jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa kasafin zai mayar da hankali kan ci gaban gidaje, aikin gona, ilimi, lafiya, da tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu, domin bunkasa tattalin arziki da samar da hanyoyin dogaro da kai ga al’umma.
Za a mika kasafin kuɗin ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin yin nazari da amincewa.
Gwamna Yusuf ya kuma sake tabbatar da niyyar gwamnatin sa ta gudanar da mulki cikin gaskiya, kula da kudade yadda ya kamata, da tallafawa dukkan sassan gwamnati domin samar da ingantattun ayyuka ga jama’a.
Idan aka amince da shi, wannan zai kasance kasafin kuɗi na farko da kowace jiha ta Arewa a Najeriya ta samar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t