Gwamnatin Kano ta bada hutun babbar Sallah ga makarantu a jihar

FB IMG 1778588658214

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta sanar da ranar fara hutun Babbar Sallah ga dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar.

A cikin wata sanarwa da Daraktan wayar da kai na ma’aikatar, Misbahu Yakasai, ya fitar ranar Laraba, an bayyana cewa daliban makarantun kwana za su fara hutu daga ranar Asabar, 23 ga watan Mayu, 2026, sannan su koma makaranta ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu, 2026.

Sanarwar ta kuma ce makarantun jeka dawo za su tafi hutun Sallah daga ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu, 2026, tare da komawa karatu ranar Litinin, 1 ga watan Yuni, 2026.

Ma’aikatar ta bukaci iyaye da masu kula da yara su tabbatar sun je sun dauki ’ya’yansu a ranar rufe makarantu tare da mayar da su a ranar da aka tsara domin komawa makaranta.

A nasa sakon, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dakta Ali Makoda, ya taya dalibai, malamai, iyaye da daukacin al’ummar bangaren ilimi murnar Babbar Sallah, tare da yi musu fatan gudanar da bukukuwan cikin zaman lafiya da annashuwa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *