Hukumar karɓar Ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta bayyana cewa ta gayyaci tsohon Shugaban Ma’aikatan jihar, Abdullahi Musa, domin amsa tambayoyi kan zargin cire kuɗaɗe daga albashin ma’aikata.
Shugaban hukumar, Sa’idu Yahaya, ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Kano ranar Talata.
Ya ce ana sa ran tsohon shugaban ma’aikatan zai gurfana a gaban hukumar cikin mako guda domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake yi masa.
Yahaya ya ƙara da cewa hukumar ta fara gudanar da bincike kan lamarin bayan samun bayanan sirri da suka shafi zargin cire kuɗin ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba.
A cewarsa, “Hukumar na binciken wasu bayanan sirri da suka shafi tsohon shugaban ma’aikatan jihar kan zargin cire kuɗaɗen ma’aikata.
“Mun gayyace shi domin ya bayyana a gaban hukumar ya amsa tambayoyi kan zarge-zargen, kuma ana sa ran zai bayyana cikin mako guda.”
Ya kuma bayyana cewa hukumar ta sanya alama a gidansa dangane da binciken da ake yi kan lamarin.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t