Gwamnatin Kano ta rufe wasu makarantu masu zaman kansu tare da gurfanar da su a gaban kuliya

FB IMG 1723959647845

Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu da na sa kai ta Jihar Kano (KSPVIB) ta dauki matakin rufe wasu makarantu guda takwas (8) da ke aiki a fadin jihar, bisa dalilai na karya dokoki da kuma sabawa ƙa’idojin gudanarwa.

Wadannan makarantu sun hada da:

1. Prime College Kano – Alu Avenue, Kano

2. Darul Ulum – Hotoro (Ahmad Musa Road)

3. Gwani Dan Zarga College – (Kofar Waika)

4. Awwal Academy – Rimi (Sumaila)

5. Dano Memorial College – (Sumaila)

6. Unity Academy – Wudil

7. Nurul Islam School

8. As-Saif College.

A yayin da yake ganawa da manema labarai, Shugaban hukumar Kwamared Baba Umar yace rufe makarantun ya zama wajibi saboda karya dokokin kara kuÉ—in makaranta da rashin yin takardun na izinin gudanarwa.

Idan za a tuna, a makon da ya gabata ne shugaban hukumar Baba Umar ya bada wa’adin mako biyu a kai korafin duk wata makaranta mai zaman kanta da ta kara kuɗin makaranta, Inda yace mutane sun bada hadin kai, su kuma sun dauki matakin da ya dace na rufe irin wadannan makarantu tare da gurfanar da su gaban kotu.

Shugaban yace a bisa umarnin Kotu, an dakatar da ayyuka a wadannan makarantun har sai abinda alkali ya yanke hukunci akai.

Yace wasu sun ƙara kuɗin makaranta ba tare da amincewar gwamnati ba.

Baba Umar ya kuma ce sun gano matsalar tsaro da rashin isasshen tsari a cikin gine-ginen wasu daga cikin makarantun.

Wasu kuma rashin ingantattun kayan aiki da guraben koyarwa da ya dace da ƙa’idar karatun zamani.

Hukumar ta bayyana cewa wannan mataki ya zama dole ne domin tabbatar da cewa yara na samun ilimi mai inganci, tare da kare iyaye daga karɓar nauyin kuɗaɗen da aka ɗora musu ba bisa ƙa’ida ba.

Ta kuma yi gargadi ga sauran makarantu masu zaman kansu a jihar da su kiyaye doka da ƙa’idojin gwamnati, inda ta ce duk wanda ya ci gaba da karya dokoki, ba za a yi masa rangwame ba.

Daga karshe ya nemi jama’a su cigaba da kai rahoton duk makarantar da ta saba doka yana mai cewa ba’a kafa hukumar sa domin kuntatawa makarantun masu zaman kansu ba sai dai domin dawo da su kan hanya idan sun kauce.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *