Gwamnatin Kano ta yi barazanar rufe makarantu masu zaman kansu kan kara kuɗin makaranta

FB IMG 1738437892655

Gwamnatin Kano ta yi barazanar rufe duk wata makaranta mai zaman kanta da ta kara kuɗin makaranta ga Iyayen yara ba bisa ka’ida ba.

Shugaban Hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ta jihar Kano Baba Abubakar Umar , ya yi wannan gargaɗin a ranar Al-hamis din nan yayin da yake ganawa da manema labarai a Kano.

Yace duk makarantar da aka samu da laifi za’a gurfanar da ita gaban kotu bayan rufe makarantar.

Baba ya ce Gwamna Abba ya dauki wannan matakin ne sakamakon koke koken da iyayen yara ke yi na karin kudin da makarantun da tsauwalawa wajen siyan littafai da kayan makaranta.

Sannan shugaban ya ce, za su fara rufe makarantun da ke biyan masu kwalin Digiri kasa da Dubu 20 da kuma masu tilasta biyan kudin biki.

Hakazalika ya bukaci iyaye da su dinga biyan kudin makaranta akan lokaci.

A kwanan nan da aka koma makaranta, iyayen yara a Kano sun koka da karin kuɗin makaranta da kuɗin littatafai da ake tursas musu saya ba bisa ka’ida ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *