Gwamnatin Najeriya Ta Ɗauki Hanyar Fitar Da ƴan Ƙasa Miliyan 100 Daga Talauci

Alfijr ta rawaito Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo, ya ce gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin samar da ayyukan yi na din-din-din ga ƴan ƙasa miliyan 21 tare da fitar da mutane miliyan 35 daga kangin talauci nan da shekarar 2025.

Alfijr Labarai

Mu’azu a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Sam Idiagbonya, ya fitar, ya bayyana hakan a ranar Juma’a a taron bita na ministoci na 2022 da ke gudana a Uyo, Akwa Ibom.

A cewarsa, fannin sufurin na kan Gwadabe na cimma kudurin gwamnati na fitar da ƴan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin talauci a cikin shekaru 10.

“Wannan shine don saka hannun jari mai yawa a kan ababen more rayuwa, tabbatar daidaito a fannin kananan sana’o’i, inganta yanayin saka hannun jari, inganta yanayin rayuwa da aiwatar da dakile sauyin yanayi.

Alfijr Labarai

“Wannan zai samar da ayyukan yi na din-din-din har miliyan 21 da kuma fitar da mutane miliyan 35 daga kangin talauci nan da shekarar 2025, ta yadda za a kafa hanyar cimma kudurin gwamnati na fitar da ƴan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10.

“Shirye-shiryen na da nufin bunƙasa harkar sufuri a ƙasar nan tare da dabarun hangen nesa na matsakaicin lokaci.

“Na san cewa dukkan ku kuna sane da waɗannan manyan manufofin, saboda sun zama tsarin bin diddigin aiwatar da ayyukanmu,” in ji Sambo.

Daily Nigerian

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *