Gwamnatin Tarayya ta amince da bayar da tallafin kuɗi na naira biliyan 4 domin taimaka wa gidaje masu rauni a cikin al’umma. Haka kuma, an ware naira biliyan 2 a matsayin bashi mara ruwa ga manoma, musamman waɗanda ke yankunan karkara, domin bunƙasa noma da cimma wadatar abinci.
Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Farfesa Nentawe Yilwada, ya bayyana wannan tsari a wajen ƙaddamar da 2025 Nigeria Humanitarian Needs and Response Plan da aka gudanar a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke Abuja ranar Alhamis.
Tsarin tallafin zai tallafa wa gidaje akalla miliyan 10 da aka raba da muhallansu, tare da mayar da hankali ga mafi raunin cikin al’umma.
Shirin bayar da tallafin kuɗi zai fara ne daga watan Fabrairu zuwa Afrilu, domin magance matsalolin gaggawa da ke fuskantar iyalai da rikici ya shafa, musamman a Arewa maso Gabas.
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news follow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ