Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Litinin A Matsayin Ranar Hutu

best seller i

Gwamnatin tarayya ta bayyana Litinin 16 ga watan Satumbar a matsayin ranar hutun Maulidi, don karrama bikin zagayowar ranar haihuwar Annabin tsira Muhammad (S.A.W).

Alfijir Labarai ta rawaito ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan, a madadin Gwamnatin tarayya, in da yayi amfani da damar wajen taya al’ummar musulmi na gida Najeriya dana kasashen ketare murnar wannan biki mai alfarma.

Ministan ya kuma bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da lokacin wajen yada halayen nagartu tsakanin abokan zama don samun wanzuwar zaman lafiya a kasa ba ki daya.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *