Gwamnatin Tarayya Ta Bankado Asirin Masu Daukar Nauyin Ta’addanci 96 A Nigeria

Alfijr

Alfijir ta rawaito gwamnatin tarayya ta bayyana haka ne a ranar Alhamis cewa, sashin kula da harkokin kudi na Najeriya, ta gano masu hannu da shuni 96, da kuma abokan hulda da masu kudi 424.

Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a yayin wani taron karawa juna sani kan yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Buhari ke yi.

Sashin tattara bayanan sirii ya bayyana kungiyoyi 123 da kuma bureaux de chanji 33 dake da alaka da ta’addanci a Najeriya, a cewar Lai Mohammed.

Alfijr

Ministan ya ci gaba da cewa binciken ya kai ga kama mutane 45, wadanda za a gurfanar da su gaban kuliya tare da kwace kadarorinsu nan ba da dadewa ba.

A nata bangaren, binciken da sashin kula da harkokin kudi na Najeriya, a shekarar 2020-2021, ya nuna masu kudi kimanin 96 na da hannu a ta’addanci a Najeriya, abokan hulda/magoya bayan masu kudi 424, da hannun kusan kamfanoni 123 da ofishin canji 33, baya ta gano mutane 26 da ake zargin ’yan fashi da masu garkuwa da mutane 7 ne.

Binciken ya yi sanadin kame mutane 45 da ake tuhuma, wadanda nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su gaban kuliya tare da kwace kadarorin su.

Alfijr

Haka kuma, daga binciken da ta yi na kaucewa biyan haraji da ke da alaka da cin hanci da rashawa, NFIU ta gano N3,909,707,678,112.43 a cikin VAT da kuma N3,737,918,335,785.82 a cikin Hana Harajin da Gwamnati ke bi.

NFIU ta kuma aike da rahotannin leken asiri guda 1,165 kan laifukan cin hanci da rashawa da halasta kudaden haram da sauran manyan laifuka ga hukumomin cikin gida guda 27 domin gudanar da bincike da gurfanar da su a gaban kotu da kuma kwato kadarori.

Slide Up
x