Gwamnatin Tarayya ta Fara Tattaunawa da kungiyar likitocin Najeriya (N A R D)

Alfijr Labarai

Gwamnatin Tarayya ta fara tattaunawa da kungiyar likitocin Najeriya kan bukatun likitocin.

Alfijr ta rawaito, sakataren Yada Labarai na NARD, Dokta Yusuf Alfa ne ya bayyana haka

Alfijr Labarai

A ranar 30 ga Yuli, 2022 ne likitoci suka ba da wa’adin makonni biyu ga Gwamnatin Tarayya da ta aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin da ta kulla da kungiyar ko kuma ta shiga yajin aiki na dindindin.

Likitocin suna rokon gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki kan biyan sabon asusun horas da ma’aikatan aikin jinya da aka sake duba domin baiwa mambobinta damar saduwa da ranar rufe rajistar jarrabawa kamar yadda kwalejin likitanci ta kasa ta bayyana; aiwatarwa

Haka  kuma biyan sabon alawus-alawus na kwarewar aiki da basussukan da ke ƙunshe a cikin daftarin da aka fitar daga hukumar Kula da ma’aikata ta Ƙasa, da biyan bashinsu na 2014, 2015, da 2016 ga membobin da suka cancanta a biya na daidaita mafi ƙarancin albashi ga membobin da aka hana su tun lokacin da aka aiwatar da shi shekaru da yawa da suka gabata.

Alfijr Labarai

Sauran bukatu sun hada da sake duba tsarin albashin Likitoci nan take da sauran alawus-alawus masu alaka idan aka yi la’akari da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki; biyan bashin albashi ga likitoci a Abia (watanni 26), Imo (watanni 10), Ondo (watanni biyar), Ekiti (watanni uku), da Gombe (watanni biyu); da sauransu.

Dakta Alfa ya ce kungiyar na ganawa da jami’an gwamnati kan bukatun ta.

“Muna ganawa da jami’an gwamnati amma ba tattaunawa kai tsaye da ta shafi kowa da kowa ba.

Muna ganawa da jami’an gwamnati game da yadda za a magance matsalolin kafin cikar wa’adin.

Alfijr Labarai

“Ya zuwa yanzu, yana da kyau, muna samun wasu amsoshi masu kyau daga wadanda muke ganawa da su amma ba a kai ga abin da muke so ba.

Akan gwamnonin jahohin da suke bin mambobinmu watannin albashi wasu sun yi alkawarin biyan wani bangare na sa amma ba a yi komai ba.

“Game da alawus-alawus na ayyukan hadari, da kuma asusun horar da Mazauna Likita, akwai ‘yan ci-gaba da ake samu duk da cewa yana tafiyar hawainiya amma za mu yi fatan an warware duk wadannan kafin cikar wa’adin mu.

“Mun sami wasu yan cigaba game da MRTF amma har yanzu batun kudin bai zo ba, ga kudaden alawus-alawus, ana ci gaba da aikin amma har yanzu ba mu ga komai dangane da biyan kudin ba,” inji shi.

Alfijr Labarai

Wakilinmu ya tuntubi Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire don jin ta bakinsa, amma bai amsa kiran waya ko sakon kartakwana da aka aika masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Kamar yadda The Punch ta wallafa