Gwamnatin Tarayya Ta Saki Ka’idojin Yin Twitter, Tik Tok, Facebook, Instagram YouTube Da Sauransu.

Alfijr

Alfijr ta rawaito gwamnatin tarayya ta fitar da ka’idar aiki don hulɗar sadarwar na’ura mai kwakwalwa, Intanet da kuma sharuddan aiki a Najeriya. Inji Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA),

Hajiya Hadiza Umar, Daraktar Hulda da Jama’a ta NITDA, ta ce dokar da aka kafa na nufin kare hakkin ‘yan Najeriya da wadanda ba ‘yan Najeriya ba da ke zaune a kasar.

A cewarta, an samar da ka’idar aiki tare da hadin gwiwar Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) da Hukumar Yada Labarai ta Kasa (NBC).

Alfijr

Ta kara da cewa, yana da bayanai daga shafukan Sabis na Kwamfuta kamar Twitter, Facebook, WhatsApp, Instagram, Google da Tik Tok da sauransu.

Sauran masu ruwa da tsaki da ke da ilimi na musamman a fannin, an tuntube su irin Kungiyoyin Jama’a da kungiyoyin kwararru, sakamakon wannan tuntuba an shigar da su cikin daftarin ka’idar aiki,” in ji ta.

Alfijr

A cewar sanarwar, sabuwar duniya ita ce ayyukan da ake gudanarwa a kan shafukan na kan layi suna da tasiri mai yawa akan al’umma, musamman mu’amalar zamantakewa, da bumksar tattalin arziki.

A cewarta, ka’idar aiki shine shiga tsakani don sake daidaita alaƙar shafukan sadarwa, tare da ‘yan Najeriya, don haɓaka amfanin juna ga al’umma, tare da haɓaka tattalin arziƙin zamani mai dorewa.

Alfijr

Hadiza ta ce kundin ya tanadi hanyoyin kiyaye tsaro da jin dadin ‘yan Najeriya yayin da ake mu’amala da shi a kan Dandalin.

Hakazalika, domin tabbatar da bin ka’idar aiki, NITDA ta kuma sanar da dukkan kamfanonin sadarwa na Intanet da ke aiki a Najeriya cewa gwamnati ta gindaya sharuddan aiki a kasar.

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa

Slide Up
x