Mafarauta Sun Kashe Uwa Da Danta Akan Zargin Kashe Al umma A Adamawa

Alfijr

Alfijir ta rawaito Mafarauta sun kashe wata mata mai suna Uzarai Musa da danta Kladang Musa mazauna yankin Bitikaya da ke karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa

Inda wasu mafarauta suka harbe su har lahira, Uzairai da Kladang ana zarginsu da maita ne.

An zargi mamatan da kashe mutane tare da sanya cututtuka ga mazauna unguwarsu tsawon shekaru.

Alfijr

Mafarautan sun yi ikirarin cewa matattun sun kashe ’yan uwansu biyu kuma su ne ke da alhakin kashe-kashe da abubuwan da ke faruwa a cikin al’ummarsu.

Mafarauta sun harbe marigayi Uzarai a ciki, yayin da danta suka harbe a wuyansa a gidansu.

Alfijr

Jami’in hukumar ‘Crack Squad’ na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, CSP Ahmed Danjuma Gombi, ya bayyana cewa jami’an rundunar sun kama wasu mutane 15 da ake zargin suna da alaka da kisan gillar kuma ana ci gaba da bincike

Kamar yadda Leadership ta wallafa

Slide Up
x