Alfijir

Gwamnonin tarayya ta dakatar da shahararriyar shirin Vision FM Idon Mikiya
Rahotanni sun ce gwamnatin tarayyar Najeriya ta dakatar da shirin saboda sukar da take yiwa gwamnatin Najeriya.
Alfijir
Hukumar gudanarwar kafafen yada labarai na Vision a yau a Abuja ta samu wasika daga ma’aikatar yada labarai ta tarayya cewa daga yanzu a dakatar da shirin tattaunawa Idon Mikiya.
Jaridar NIGERIA TRACKER ta tabbatar da hakan ta hannun daya daga cikin manajojin Vision Fm Shu’aibu Mungadi
Alfijir
Ya ce hukumar ta Vision Media ta kuma samu wani umarni daga hukumar leken asiri ta kasa ta daina ci gaba da watsa Idon Mikiya.
Idon Mikiya shiri ne mai farin jini wanda manyan ‘yan jaridu da masu gidan rediyon Vision FM daga Abuja ke gabatarwa wanda suka hada da Umar Faruk Musa, Shuaibu Mungadi, Abubakar Kabiru Matazu.
Alfijir
Ana watsa shi a ranakun Litinin, Talata da Alhamis a tashoshi 7 na ayyukan yada labarai na Vision a fadin Najeriya.
Tattaunawar shirin ta ta’allaka ne kan harkokin mulki, kashe kudaden gwamnati da suka hada da bin diddigin kasafin kudi da kuma rashin tsaro da al’umma ke yi.