Alfijir

Alfijir ta rawaito CNN ta sanar da sanya gidajen yarin tarayya na wucin gadi a duk fadin kasar a ranar Litinin bayan tashin hankali ya barke a wata cibiya a Texas kuma fursunoni biyu sun mutu.
Hukumar da ke kula da gidajen yari ta tarayya (BOP) ta ce tana yin taka tsantsan kuma za a kiyaye wuraren a matsayin “matakin wucin gadi na tabbatar da kyakkyawan tsarin cibiyoyinmu, muna tsammanin wannan matakin na tsaro zai kasance na dogon lokaci.
Alfijir
Hukumar ta ce a cikin wata sanarwa da ta fitar an gwabza fada jiya litinin jim kadan da tsakar rana CT wanda ya hada da fursunoni da dama a gidan yari na Amurka Beaumont da ke kudu maso gabashin Texas.