Hanyoyi 14 Da Zaki Bi Don Zama Uwa Ta Gari kenan

    Alfijr na taya mata murnar zagayowar wannan rana mai albarka, Allah ya karawa Iyayenmu lafiya da daukaka wadanda suka mutu Allah ya jikan su.

1. kamewa:

Daga dukkan wani abu da zai sosa wa maigidanta rai, a kanta ne ko gidansa ko abincinsa da sauransu.

    2. Gaskiya:

Idan mace za ta yi magana kar tayi karya, domin samun mallakar gidan baki daya.

    3. Amincewa:

Duk abin da mai gidanta yake so to ta amince, don tana da yakin in cewa ba zai cutar da ita ba.

    4. Tawalu’u

Ta zama mai kankar da kai ga mai gidanta koda kuwa tana da ilimi, arziqi da shekaru sama da shi, kamar dai Khadeejah R.A da Annabi (S.A.W)

     5. Nutsuwa:

Kar mace ta rinka tuno abubuwan da suka faru a baya, kuma karta tsoron abun da zai zo na gaba.

    6. Kunya:

Mace ta zamo mai jin kunya, wannan ado ne gare ta, masamman in tana tare da shi a cikin jama’a, wannan zai kara masa kaunarta.

    7. kwanciyar Hankali

Mace ta zamo mai mantawa da matsalolin rayuwa da kokarin saka farin ciki ga mai gida koda suna cikin matsala.

    8. Godiya:

Duk abin da mai gidanta ya zo da shi a nuna masa jin dadin zuwa da shi komai girmansa komai kankantarsa.

   9. Hakuri

Mace ta yi hakuri akan duk abin da zai bayyana daga miji mai dadi ko mara dadi.

   10. Tsayuwa Kyam:

Mace ta zama mai bauta Allah da kulawa da miji da yayansa tare da dangunsa

    11. Amana

Mace ta zama mai amana, kar ta yarda maigidan ta ya ga ha’incinta koda kuwa sau Daya ne, ta rika gaya masa abin da za ta yi domin maganin shedan.‎

     12. Cika Alkawari

Yana Daya daga adon mace da namiji.

     13. Tsoron Allah

Mace ta kasance a duk abin da za ta yi ta saka Allah a gaba.

     14. Danne Zuciya

Mace ta zamanto mai danne zuciyarta yayin da aka bakanta mata rai

Slide Up
x