Kamfanin Burtaniya, Kingston Organic, Ya Na da Sunusi Bature Jakadan Ayyuka A Nijeriya

Alfijr

Alfijr ta rawaito hukumar gudanarwar Kingston Organic Plc, da ke Kasar Ingila ta nada Sunusi Bature Dawakin Tofa a matsayin mataimakin shugaban aiyuka a Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a California, kasar Amurka ta hannun babban jami’in gudanarwa na kamfanin Mista Maurice Frosch.

Mista Frosch ya ce nadin Sunusi Bature a matsayin shugaban ofishin hadin gwiwa na yammacin Afirka a matsayin mataimakin na musamman zai fara aiki daga ranar Talata 1 ga Maris, 2022.

Alfijr

Kuma za su yi aiki a matsayin yarjejeniyar haɗin gwiwa tsakanin bangarori uku, tsakanin wani shahararren kamfanin kasuwanci na Najeriya Silvex International Limited, RegenFarm UK da Kingston Organic Plc.

Sunusi Bature ƙwararren dan jarida ne, wanda ya ƙware a fannin sarrafa ayyukan, sadarwa na cigaban, bunƙasa kasuwanci, dabarun tallace-tallace na kamfanoni tare da ƙwarewar aiki kusan shekaru ashirin

A cikin shekaru 18 da suka gabata, ya gudanar da ayyuka daban-daban da shirye-shirye dangane da harkokin noma, shugabanci, ilimin yara da mata, kula da lafiyar mata da yara, ƙarfafa rayuwa.

Alfijr

Shi ne wanda ya lashe lambar yabo ta ilimi a Cambridge kan aikin jarida a shekarar 2008.

Bature ya yi aiki a wurare daban-daban da kungiyoyi da dama kamar Ofishin harkokin waje da kasuwanci na Biritaniya (FCDO), hukumar bunkasa cigaba ta Amurka. (USAID), da sauransu.

Ya rike mukamai da dama da suka hada da General Manaja, Director, ya sake yin general Manaja daga bisani ya sake zama mataimakin Darakta Ayyuka, dukkannin wadannan mukaman ya samesu ne a ma aikatu daban daban na gida dana kasashen waje.

Alfijr

Sanusi ya kammala digirinsa na farko (B.A. Hons.) a Mass Communication a Jami’ar Maiduguri, ya yi Diploma kan Mass Communication a Kaduna Polytechnic, sai babbar Diploma (HND) da Diploma na Postgraduate a fannin Ilimin Kiwon Lafiyar Jama’a da cigaba. Ya kuma samu MSc. a cikin Ayyukan zamantakewa tare da ƙwarewa a cigaban al’umma daga Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola, (LAUTECH) Ogbomosho, Jihar Oyo da kuma wani digiri na biyu a Harkokin Jama’a (MPR) daga Jami’ar Bayero mai daraja, Kano, Nigeria.

Alfijr

Ya shiga cikin shirin digiri na biyu akan Gudanar da Ayyuka a Kwalejin Robert Kennedy, Zurich, Switzerland.

Slide Up
x