Hukumar Hisba Ta Cafke Wasu Bayin Allah Suna Yin Zina A Bainar Nasi

Alfijr ta rawaito Hukumar Hisbah ta Jahar Zamfara tayi Nasarar cafkesu mace da namiji tare da Gurfanar dasu a Gaban Kotun Shari’ar Musulunci dake Kan wuri Gusau.

Alfijr Labarai

Wani ganau ya shaidawa Alfijr cewar, kafin dai su fara wannan aika-aika a cikin wannan babbar tashar garin Gusau, musu ne ya kaure a tsakaninsu kan cewa ya fita iskanci ita ma tace ta fishi iskanci, daga nan sai suka yi yarjejeniyar cewar  dukkanin su suyi zigidir, hakan kuwa akayi, daga bisani kuma ta umarce shi da ya hau ruwan cikinta ya fara lalata da ita a Gaban jama a

Shi ko gogan naka bai yi wata wata ba ya dare bisa kanta, suka ci gaba da sha aninsu abinsu kamar suna cikin daki

Suna cikin wannan badalar ne sai jama a suka sanar da Hukumar Hisba, nan ba nan sai gasu sun garzayo suka tarkatasu sai ofishinsu.

Alfijr Labarai

Bayan gudanar da bincike hukumar ta gudanar da su a gaban kotun musulunci da ke Kan Wuri a birnin Gusau,

Da ya gabatar dasu gaban mai sharia Dan Sanda Lawal Abubakar Muradin ya gabatar dasu gaban kotu.

Ko da karanta musu kunshi tuhumar da ake musu babu musu suka amsa.

Alfijr Labarai

Ko da manema labarai suka waiwayi  wadanda ake tuhumar, sai macen ta ce, “Ni wallahi ba aikina bane, sanduna nake siyarwar a tashar idan ban sami ciniki ba  haka nake hakura, wannan kuma sharrin  shedan ne”

A na sa batun abokin burmin nata mai Suna Murtala ya ce, A gaskiya ni ban san yadda hakan ta faru ba ma, don na biya ta wani gidan biki na sha wani lemo, wata kila wannan ne aka saka abin buguwa cikin hankali ya gushe mai afkuwar ta afku.

Alfijr Labarai

Da karshe dai mai sharia ya aike dasu gidan gyaran hali da tarbiyya zuwa zama na gaba

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *