Hukumar Hisbah Ta Cafke Mutume 78 Bisa Zargin Hada Auren Jinsi A Kano

Alfijr

Alfijr ta rawaito, hukumar ta cafke mutane 78 da ake zarginsu da hada auren jinsi

Alfijr

Sumamen ya faru ne a unguwar Nassarawa GRA a wani gida da ya yi kaurin suna wajen aikata masha’a da ake kira ‘White House’ dake unguwar.

Jaridar Aminiya ce ta sanar cewar Hisban ta kai samame gidan ne in da suka sami maza da mata cakude ana casu, gefe guda kuma ga kororon roba da suka jibge.

Alfijr

Bayanan dai sun ce Hisbah ta cafke mutum 78 yayin da wasu kuma suke tsere, hukumar a yanzu haka tana gudanar da bincike a kai.

Matasan wadanda suka musanta zargin, sun ce suna casun bikin murnar zagayowar ranar haihuwar daya daga cikinsu ne.

Alfijr

Rahotanni sun ce ko a shekarar da ta gabata sai da hukumar Hisbah ta cafke wasu matasa maza da ake zargi da yunkurin daura auren jinsi, wanda shi ma a wancan lokaci suka musanta.

Slide Up
x