Alfijr ta rawaito Dakarun Hukumar Hisbah a jihar Jigawa sun kama mutane 31 da su ka haɗa da mata 25 a Ƙaramar Hukumar Kazaure da ke jihar a yau Laraba, bisa zargin su da laifin aikata masha a.
Alfijr Labarai
Kwamandan Hisbah a jihar, Ibrahim Dahiru, ya ce an kama wadanda ake zargin ne da misalin karfe 6 na safe bisa zargin karuwanci da shan barasa.
Ya bayyana wa manema labarai a garin Dutse a yau Laraba cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani samame da hukumar Hisbah ta kai mai taken: “Abin da ka shuka shi za ka girba”.
Kwamandan ya ce an kama kwalabe 55 na barasa kala kala da kuma lita 50 na Burukutu’ a yayin farmakin.
Ya kara da cewar, an mika wadanda ake zargin da kayayyakin da aka kama ga ‘yan sanda a yankin domin ci gaba da daukar mataki.
Alfijr Labarai
Dahiru ya yabawa al ummar jihar bisa goyon bayan da suke baiwa hukumar Hisbah wajen gudanar da ayyukanta.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa Hisbah za ta ci gaba da yaki da munanan dabi’u a duk sassan jihar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller