Hukumar Hisbah Ta Kano Ta Kama Wasu Motoci Makare Da Barasa

Alfijr

Alfijr ta rawaito, hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu motoci hudu dauke da kwalaben barasa sama da 4,200.

Babban kwamandan hukumar Dr Harun Ibn Sina ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano ranar Asabar.

Alfijr

A cewarsa, an tare motocin ne a hanyar Kwanar Dangora-Kiru Madobi da kuma hanyar Zariya zuwa Kano.

Kwamandan Janar din ya bayyana cewa, dokokin shari’ar jihar Kano sun haramta sha da sayar da barasa da sauran abubuwan sa maye sannan kuma ta kebe takunkumi mai tsauri ga duk wanda aka samu da laifin.

Alfijr

Hakazalika, ya ce hukumar ta samu nasarar cafke wasu bata gari da ke yin karuwanci, da muggan kwayoyi da sauran haramtattun ayyuka a Panshekara.

Ibn Sina ya ce an kama matasan maza da mata ne bayan sun samu koke daga mazauna yankin.

Alfijr

Ya koka kan karuwar kararrakin matasa masu karancin shekaru da ke aikata munanan dabi’un al’umma wadanda galibi ke kai ga aikata laifuka.

Babban Kwamandan ya bukaci ‘yan jihar da su kara sanya ido tare da kai rahoton duk wani mutum da ake zargi da shi ga hukumomin da abin ya shafa.

Alfijr

Ya kuma tabbatar da shirin hukumar na hada hannu da masu ruwa da tsaki wajen kawar da duk wata munanan dabi’u a jihar.