Alfijr
Alfijr ta rawaito, a kalla mutane shida ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a unguwar Tungan Maje da ke babban birnin tarayya Abuja.
Alfijr
Har ila yau, an ce mutane 9 ne suka jikkata a hatsarin wanda ya faru da misalin karfe 10 na safiyar ranar Juma’a.
Wani ganau mai suna Austin, ya ce hatsarin ya faru ne a sanadiyyar wata babbar motar dakon kaya, inda daga bisani ta kutsa cikin wata motar haya.
Alfijr
Ya kara da cewa mutane biyar ne suka mutu nan take yayin da wani fasinja ya mutu a kan hanyar zuwa asibiti, inda ya ce uku sun tsira ba tare da jikkata ba.
Ya kara da cwar, hatsarin ya yi muni sosai kuma wurin ya kasance mai ban tsoro, ya hada da motar haya da babbar mota.
Da farko biyar sun mutu nan take amma daya daga cikin wadanda suka jikkata ya mutu a kan hanyarsu ta zuwa asibiti, mutane uku ne suka yi sa’a, sun fito ba tare da jin rauni ba.
Alfijr
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa FCT, Ogar Ochi, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya kara da cewa gudun wuce gona da iri ne ya haddasa hatsarin, ya ce, mutane 18 ne suka yi hatsarin, an tabbatar da mutuwar mutane 6, yayin da wasu tara suka mutu. wanda ya samu rauni, hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce gona da iri. Inji kwamandan