Alfijr ta rawaito Hukumar da ke yaki da cin hanci a Nijeriya ICPC za ta fara bin diddigin wasu ayyuka 712 na ‘yan majalisun tarayya a jihohi 20 na kasar.
Mai magana da yawun hukumar Azuka Ogugua ta sanar da hakan a Abuja, inda ta ce za a gudanar da wannan bincike ne a jihohin Katsina, Kaduna, Jigawa, Sokoto, Kwara, Niger, Kogi, Cross Rivers da Delata.
Sauran su ne Rivers, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Anambra, Enugu, Abia, Borno, Bauchi, da Gombe.
Azuka ta ce wannan tsarin zai tabbatar da bin diddigin ayyukan raya kasa da aka ba da kwangilar su a duk fadin kasar da tabbatar da an gudanar da su a inda aka tsara tun farko.
Mai magana da yawun hukumar, ta ce a baya an gano kudi N7.1bn da aka yi cushenta a cikin ire-iren wadannan ayyukan, wasu ‘yan kwangilar kuma sun yi watsi da ayyukan.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux