Hukumar Karota Ta Sake Kama Wata Tirela Maƙare Da Giya A Kano

Alfijr ta rawaito akaro na biyu ƙasa da mako guda, Hukumar kula da Zirga-zirga ababen hawa ta jihar Kano KAROTA karkashin shugabancin Baffa Babba Dan’agundi taƙara nasarar cafke wata mota ƙirar Tirela maƙare da Giya a cikinta Akan Hanyarta na Shigowa cikin Birnin kano.

Alfijr Labarai

Hukumar ta Karota tasami nasarar cafke Tirelar ne a kan titin Bello Dandago da misalin karfe 2:30 na daren Larabar da ta gabata, a ƙoƙarin su na shiga cikin Anguwar Sabon Gari, amma jami’an na Karota sukayi nasarar cafke motar a lokacin da suka buƙaci direban motar ya gabatar musu da takardar shaidar abinda ya ɗauke dashi na Way bill, Sai Dreban ya bayyana musu cewar Kwali ya ɗakko, Bayan da jami’an suka matsa masa da bincike sai suka gano cewar giyace a cikin babbar motar ba kwali ba.

Idan Buku manta ba Shugaban Hukumar ta karota Baffa Babba Ɗan’agundi ya bayyana cewa Hukumarsa ta KAROTA baza taba gajiya ba wajen kama duk wani nau’in kayan da dokar jihar Kano bata amince da’a shigo dasu ba tare mekasu hannun da Hukumar datake da alhakin Abin.

Ya kuma ƙara da cewar zai ƙara baza jami’ansa na fili dana boye Musamman kan manyan titinan jihar kano domin ganin an daƙile shigowar kayayyakin da dokar jihar Kano bata aminta da shigowa dasu ba,

Baffa ya kumace da zarar an kammala bincike za a miƙa giyar zuwa ga hukumar Hisbah domin ɗaukar mataki na gaba.

Slide Up
x