Wata Kotu Ta Aike Da Wasu Teloli 2 Da Abokan su 3 Gidan Gyaran Hali

Alfijr ta rawaito Mai shari’a Ibrahim Yusuf na babbar kotun jihar Kwara, dake Ilorin ya yanke wasu teloli biyu: Jatto Mujeeb, Opeyemi Bhadmus Abdulsamad, tare da wasu mutane uku da suka hada da: Ipadeola Olawale, Tomiwa Kingsley da Kolawole Segun hukuncin zama gidan gyaran hali.

Alfijr Labarai

An yanke musu hukuncin ranar Litinin, 29 ga watan Augusta, 2022 bayan sun amsa laifuka da hukumar EFCC ta tuhume su masu alaka da zamba da cin amana.

Mai shari’ar ya yanke wa Mujid hukuncin watanni shida ko ya biya tarar Naira dubu hamsin, haka ma Bhadmus zai yi zaman watanni shida ko ya biya tarar Naira dubu dari.

Olawale ma zai yi watanni shida ko ya biya tarar Naira dubu dari.

Alfijr Labarai

Haka ma Kingsley zai yi watanni shida akan duk tuhumar da aka mishi ko ya biya tarar Naira dubu dari.

Sai Segun da zai yi watanni shida yana hidimar al’umma ba tare da biyan tara ba.

Slide Up
x