Hukumar Kiyaye Hadaruka FRSC Ta koka Kan Tukin Ganganci Dake Karuwa A Titin Kano Zaria

Alfijr

 Hukumar kiyaye hadari ta kasa FRSC reshen jihar Kano, ta ce titin Kano zuwa Zaria ya kasance wurin da hukumar ke fuskantar kalubalen masu ababen hawa, yadda suke tukin ganganci a kan hanyar da a halin yanzu ake gyarawa.

Zubairu Mato wanda shine babban kwamandan hukumar FRSC ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Ya kuma koka da yadda masu ababen hawa da ke bin hanyar suna gudun wuce gona da iri, wanda hakan kan haifar da munanan hadari a hanyar.

Alfijr

Mato ya ce, ya tura jami’ansa kan hanyar da kayan aikinsu domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kwamandan ya cigaba da cewa rundunar ta samu nasarar tantance hadurran da ba a taba samu ba a kan hanyar Kano zuwa Bauchi da Kano zuwa Azare da dai sauransu.

Slide Up
x