Jarumar Kannywood, Nafisa Ishaq Ta Magantu Kan Matsalar Ta Da Malam Daurawa

Alfijr ta rawaito Nafisa Ishaq jarumar masana’antar fina-finai ta Kannywood, ta roƙi mal Aminu Daurawa da ya yafe mata a kan fefen bidiyo da ta yi ta caccaba masa magana ta kafar tiktok.

Malam Daurawa yayi wani karatu ne a kwanakin baya inda yake cewa mafi kazanta a jikin mace, al’aurarta, saboda ta nan take fitsari take al ada.

Wannan karatu, da jama’a da dama, musamman mata su ka yi wa mummunar fahimta, ya janyo kace nace a kafafen sadarwa a tsakanin mata.

Alfijr

Nafisa, na daya daga cikin wacce ta yi faifen bidiyo ta na maida wa Malamin martani, sai dai daga baya jarumar ta nuna nadamarta, ta na baiwa Mal Daurawa haƙuri, ta ce “sharrin shaiɗan ne .Dan Allah Malam ka yafe mini, al’ummar Musulmi kuma ku yafe min na tuba, inji Nafisa.

Slide Up
x