Ibtila in Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutum 51 A Jigawa

Alfijr ta rawaito Mutanen 51 da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Jigawa

Babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA, Sani Yusuf ne ya bayyana wa gidan talabijin na Channels afkuwar hakan.

Sani ya ce, mutum sama da 2,051 ambaliyar ta daidaita a kauyen Karnaya da ke Dutse, babban birnin jihar. Jigawa

Ya Ζ™ara da cewa, gwamnatin jihar na shirin kai iyaye 404 da ‘ya’yansu da suka kai 1,334 zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na Warwade, yayin da maza 313 kuma za su ci gaba da zama a wata makarantar firamare da ke kauyen kafin ambaliyar ta ragu.

Alfijr Labarai

Babban sakataren ya kara da cewa suna kuma bukatar agaji saboda ambaliyar na ci gaba da shiga kauyuka, inda gadoji da dama suka karye, inda ya gargadi direbobi da su kiyaye yayin tuki.

Ya kuma ce gwamnatin jihar ta mikawa gwamnatin tarayya wnai rahoto, inda take bukatar taimako wajen takaita ambaliyar ruwan.

BBC Hausa

Slide Up
x