Wata tankar mai dauke da fetur ta fashe a yankin Maitama da ke Abuja, a daren ranar Litinin, lamarin da ya jikkata mutane da dama tare da haddasa firgici.
Alfijir Labarai ta rawaito lamarin ya faru ne a kan titin Shehu Shagari, wanda hakan ya jikkata mutane da dama, ciki har da fasinjojin motar haya.
Shaidu sun bayyana cewa wajen da lamarin ya faru ya cika makil, yayin da jami’an agajin gaggawa suka yi sauri zuwa domin kai dauki.
Lamarin ya sanya an sanar da asibitoci da ke kusa da yankin don kai daukin gaggawa.
Wani ma’aikacin kiwon lafiya a Asibitin Gundumar Maitama ya tabbatar da cewa ana kula da wadanda suka jikkata.
Leadership Hausa
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj