Daga Aminu Bala Madobi
Kwamitin karɓar Ƙorafe-ƙorafe kan Kafafafen Yaɗa Labarai na Kasa (NMCC), ya fitar da rahotonsa kan taƙaddamar zargin goyon bayan auren jinsi a yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta sanyawa hannu ta Samoa.
Alfijir Labarai ta rawaito kwamitin wanda gogaggun yan jarida da lauyoyi ke yiwa shugabanci ya, ce kamfanin Daily Trust ya tafka kuskure a wancan labarin akan yarjejeniyar ta Samoa.
Binciken ya biyo bayan korafin da Ma’aikatar Yada Labarai da wayar da Kan Jama’a ta Najeriya ta yi a kan jaridar Daily Trust.
Hukumar, a cikin rahotonta mai shafuka 19, ta ce bayan ta binciki korafin gwamnati, da kuma martanin da jaridar tayi, ta gano labarin da jaridar Daily Trust ta wallafa kan yarjejeniyar Samoa a matsayin kuskure, tare da umartar Jaridar ta nemi afuwar Gwamnatin Tarayya bisa abin da rahoton na su ya jawo mata.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇