Ibtila’i! Mutum 10 sun mutu wasu sun jikkata a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Shinkafa

Aƙalla mutum 10 ne sun rasa rayukansu, wasu kuma da dama sun jikkata yayin wani turmutsutsi da ya faru a Cocin Holy Trinity Catholic Church da ke Maitama, Abuja, a ranar Asabar.

Rahotanni, sun bayyana cewa turmutsutsin ya faru ne lokacin da ake raba tallafin abinci a cocin da sanyin safiyar asabar.

Rundunar  yan sandan Abuja, ta tabbatar da aukuwar lamarin tare da adadin waɗanda suka mutu.

Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta ce yara huɗu na daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu.

Hakazalika, ta ce mutum takwas sun samu raunuka daban-daban.
“Mutum huɗu daga cikin waɗanda suka jikkata an sallame su bayan samun kulawa a asibiti,” in ji SP Adeh.
Bayanai, sun nuna cewa an shirya rabon tallafin ne don taimaka wa mabuƙata yayin shirin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Wasu da suka shaida faruwar lamarin, sun ce turmutsutsin ya faru ne da misalin karfe 7 na safiyar ranar Asabar.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *