Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana dan takarar jam’iyyar NNPP , Alhassan Ishaq, a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Kura/Garun Mallam a jihar Kano.
Alfijir labarai ta rawaito Baturen zaben na INEC Farfesa Shehu Galadanchi ya bayyana cewa Ishaq na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 37,262 inda ya doke Hayatu Musa Daurawa sallau na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 30,803.
Idan dai za a iya tunawa kotun daukaka kara ce ta umarci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfuna 20 na mazabar Kura/Garun Malam a jihar Kano.
Haka kuma, INEC ta ayyana Bello Butu-Butu na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Rimin Gado/Tofa.
Babban Baturen zaben Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ya sanar da cewa Bello Butu-Butu na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 31,135 inda ya doke abokin takararsa na APC wanda ya samu kuri’u 25,577.
Kotun daukaka kara ta kuma umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 33 a mazabar Rimin Gado/Tofa dake jihar kano.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V