Jam iyyar ADP Ta Kori Koguna Saboda Ƙin Biyayya Ga Takarar Shaaban Sharada

Alfijr ta rawaito jam’iyyar Action Democratic Party, ADP, ta kori Nasiru Koguna, ɗan takararta na gwamna a Kano, saboda ƙalubalantar maye gurbinsa da Hon Shaaban Sharada.

Alfijr Labarai

Da farko dai an zaɓi Koguna a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar kafin a ce ya janye wa Shaaban.

A cikin wata wasiƙa da ta aike wa Koguna, mai ɗauke da sa hannun sakataren jam’iyyar na kasa, Victor Fingesi, ADP ta ce ta kafa kwamitoci biyu domin warware rikicin Kano, tare da sasanta ƴaƴan jam’iyyar, amma ya ƙi amsa gayyatar.

Ganin yadda ya kasa kare kansa da zargin rashin ɗa’a, rashin biyayya, kalaman ɓatanci ga jam’iyyar da shugabanninta, don haka jam’iyyar ta sallame shi daga clkinta

Alfijr Labarai

Don haka, bisa ga sashi na 52 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar Action Democratic Party, kwamitin gudanarwa na kasa, bayan nazari da duba na tsanaki kan rahoton waɗannan kwamitoci guda biyu, ya yanke hukunci kamar haka:

“Wannan bisa la’akari da rashin ɗa’a, rashin biyayya, kalaman ɓatanci ga jam’iyyar da shugabanninta, kamar yadda yake a cikin sashe na 52.2 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar, don haka an kore ka daga matsayin ɗan jam’iyyar Action Democratic Party, ADP, daga yau. 9 ga Satumba, 2022.

“Bisa ga haka, kai (Nasiru Hassan Koguna) ba za ka sake nuna kanka a matsayin ɗan jam’iyyar ADP ba, kuma ba za ka iya wakiltar jam’iyyar a kowane matsayi ba,” in ji wasikar.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *