Gwamnatin Kano. Ta Rusa Chamber Of Commerce, Ta Kafa Kwamitin Riko

Alfijr

Alfijr ta rawaito gwamnatin jihar Kano ta ba da umarnin rusa shugabannin kungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adinai da noma ta Kano (KACCIMA), ba tare da bata lokaci ba, saboda rashin shirya sabon zabe

Musa Tanko, Jami’in Hulda da Jama’a na Ofishin Majalisar Dokokin Jihar Kano ne ya bayyana haka a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, ranar Laraba a Kano.

Tanko ya ce sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanya hannu kan wannan umarnin.

Alfijr

Ya kuma bayyana cewa, ya zama wajibi a dauki matakin ne sakamakon gazawar da shugabancin hukumar ta KACCIMA mai ci a yanzu ta shirya sabon zabe mai karbuwa, tun bayan karewar wa’adinsa.

Ya ce tuni Gwamna Abdullahi Ganduje ya amince da kafa kwamitin riko mai mutum tara, karkashin jagorancin fitaccen dan kasuwa Alhaji Lawan Garo.

Alfijr

Ya zayyana wasu daga cikin sharuddan kwamitin da suka hada da; shirya zaben cikin watanni shida, tare da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a zauren majalisar.

Ya ce mambobin kwamitin sun hada da Amb. Muktari Gashash, co- chairman, Dr Salim Muhammad, wakilin ma’aikatar kasuwanci, da Alhaji Yakubu Uba. Sai kuma Alhaji. Tijjani Usman, Alhaji. Kabiru Kura, Hajiya Aisha Baffa da Alhaji Bashir Dado, Bauran Gaya.

Alfijr

A cewar Tanko, Garo, wanda ya yi magana a madadin sauran mambobin kwamitin, ya nuna jin dadinsa ga gwamnati bisa amincewar da aka yi musu; ya kuma yi alkawarin za su yi aiki tukuru domin cimma burin da aka sanya a gaba a cikin wa’adin da aka kayyade.

Slide Up
x