Jirgin Azman Ya Dakatar Da Zirga Zirgarsa A Jihar Kaduna Ta Najeriya

Alfijr

Alfijr ta rawaito kamfanin jrgin saman Azman ya dakatar da zirga-zirga a jihar Kaduna a Najeriya

Idan zaku tuna kwanaki kadan bayan harin da wasu ‘yan bindiga suka kai filin jirgin saman jihar inda suka kashe masu gadi da wasu ma’aikata, suka kuma hana jirgin tashi

Kamfanin ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa zai dakatar da zirga-zirga a Kaduna daga ranar Litinin din da ta wuce.

Alfijr

Kamfanin ya ce ya daukar matakin ya biyo bayan yanayi na tsaro a filin jirgin saman.

Binciken da alfijr ta gudanar da safiyar talata, ta tabbatar da cinkoson matafiya a filin sauka da tashin na Kaduna saboda karancin jiragen, ga kuma matafiya sun kara karuwa duba da harin bom da aka kaiwa jirgin kasa a hanyar Abuja Zuwa Kaduna a daren Litinin.

Alfijr

Allah ya kawowa ƙasarmu lafiya da zaman lafiya baki daya amin